Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Masarautar Gidan Igwai ta dakatar da Usman Umar wanda akafi saninsa da (SOJA BOY) daga sarautar Yariman Gidan Igwai dake jihar Sokoto da Masarautar ta bashi a baya.
A wata sanarwa da ta fito daga Marafan Sarkin adar, mai dauke da sa hannun Alhaji Abubakar Marafan, Masarautar ta ce ta tube rawanin Sojaboy saboda wasu dalilai da suka bayyana.
A cewar Sanarwar ‘An samu bidiyon sa yana aikata abubuwan da suka sabawa addini, al’ada da dabi’un mutanen Gidan Igwai. Bisa wannan dalili ne masarautar ta yanke hukuncin dakatarwa tare da tsige shi daga sarautarsa.
Hakazalika, Sanarwar ta bayyana irin yadda al’ummar yankin su yi tir da wannan dabi’a kuma sun nesanta kansu daga wannan abu mara kyau. Da tsohon basaraken yake aikatawa a wakokinsa.
Daga karshe masarautar tayi nasiha ga tsohon basaraken akan yaji tsoron Allah ya rungumi dabi’u irin na karantarwar addinin Musulunci.
A kwanakin baya ne hukumar tace fina-fina ta jihar Kano ta ce ta dakatar da Sojaboy saboda wasu bidiyoyi na badala da ya ke yadawa da sunan wakoki ko fina-finan Kannywood.