Kananan Hukumomi 774 na fadin Najeriya na fuskantar barazanar rasa samun kudadensu na wata-wata kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.
Jaridar Hotpen ta wallafa cewa, babban bankin Najeriya (CBN) ya bukaci kowacce daga cikin kananan hukumomi 774 ta ba shi cikakken bayani dangane da yadda suka sarrafa kudadensu na shekaru biyu da suka gabata a matsayin sharadi kafin a tura musu kudadensu kai tsaye.
Tun a watan Janairun da ya gabata ne dai aka shirya fara biyan kudaden kananan hukumomin Najeriya kudadensu kai tsaye, amma aka dage daga karshe saboda da yawa daga cikin kananan hukumomi sun kasa gabatar da cikakkun bayanan da ake bukata domin biyansu.
- ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Budurwa Daga Hannun Matsafa A Abuja
- ‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Aiwatar Dokar Inshorar Motoci
Tuni dai babban bankin kasar ya fara shirin bude asusun ajiya ga kananan hukumomin domin samun damar karbar kason su kai tsaye daga Abuja karkashin ikon cin gashin kai da gwamnatin tarayya ta nema musu daga kotun koli.
Rashin kyakkyawan shiri ya janyo dole babban bankin Najeriya ya bai wa gwamnatocin jihohi Naira biliyan 361.754 daga kudaden shigar da ya dace a raba musu na wata-wata daga cikin Naira Tiriliyan 1.424.
Wata majiya daga CBN sun shaidawa jaridar The Nation cewa bankin ba zai iya bude asusu ga kananan hukumomin ba, ba tare da cikakken fahimtar halin da suke ciki dangane da yadda suke kashe kudadensu ba a halin yanzu.
“Ba za mu iya bude musu asusu ba yanzu, tunda yawancinsu ba su yi aiki a matsayin wata hukuma mai zaman kanta ta gwamnati ba,”
Majiyar ta kara da cewa bayanin yadda suke kashe kudaden su nada muhimmanci kwarai da gaske.