An Yanke Wa Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan gilla da aka yi wa wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na Jihar Bauchi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara shari’ar Musa ne a farkon watan Agustan 2025 bayan kama shi biyo bayan binciken haɗin gwiwa da jami’an sojoji sashin harkokin da hukumomin yankin suka gudanar.

Al’amarin ya ja hankalin jama’a sosai saboda tsananin mugun halin da aka aikata da kuma yunkurin tauye amanar jama’a da sojan ya yi.

Shugaban Kotun Sojojin Najeriya ta 3, Birgediya-Janar, Liafis Bello ya ce an samu sojan da laifin kisan kai da kuma mallakar harsasai ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun ta tabbatar da cewa, shaidun da aka gabatar a lokacin shari’ar sun nuna cewa, Musa ya haɗa baki da wani mai suna Mista Oba, domin su kai Isa gidansa da zargin taimaka masa wajen kwashe kayansa.

Ya ƙara da cewa Musa ya bugi Isa a kai da wani abu na katako, inda ya sume, kafin ya shaƙe shi ya mutu.

A ƙoƙarinsu na ɓoye laifin, Musa da abokinsa sun cusa gawar wanda aka kashe a cikin buhu tare da jefa ta a tsakanin ƙauyukan Shira da Yala a Jihar Bauchi.

“An sayar da babur mai ƙafa uku na Isa daga baya, wanda ya ƙara fallasa yadda aka tsara yadda lamarin ya faru,” in ji masu gabatar da ƙara na soji yayin shari’ar.

Hakazalika sun bayyana cewa a binciken da ake yi, an samu Musa da harsashi na musamman har guda 34 na nau’in 7.62mm ba tare da wata izinin doka ba.

Da yake yanke hukuncin, Birgediya Janar Bello ya bayyana abin da Musa ya yi a matsayin “abin kunya, rashin tausayi da kuma cin zarafi da rahin a ɗa’a da kimar sojoji.”

“Ka nuna rashin tausayi daga mai kare ’yan ƙasa zuwa mai kisan gilla, matakin da kuka ɗauka abin kunya ne kuma abin kunya ga Sojojin Najeriya,” in ji kotun.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda