Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi.
Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar.
Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Mohammed Jatau, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da wasu kwamitoci biyu kan yaki da cutar a jihar.
Mataimakin Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda barkewar cutar ke ci gaba da kashe mutane, lalata rayuwar jama’a, da kuma jefa tsarin kiwon lafiya na jihar cikin matsala.
Jatau ya bayyana cewa: “Ana iya kaucewa wannan barkewar cutar idan aka ɗauki matakan gaggawa, aka haɗa kai wajen tunkarar cutar, tare da ci gaba da inganta ruwa, tsafta da kula da muhalli. Jihar Bauchi ta samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar, tare da mutuwar wasu 58.”
Ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi, Kwalara na ci gaba da zama barazana ga lafiyar jama’a.
- An Yanke Wa Soja Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
- Za A Rataye Sojan Najeriya Saboda Halaka Ɗan Keke Napep
Ya ce kafa kwamitin yaki da cutar ba wai kawai ya zo a kan lokaci ba, har ma yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin da aka sa gaba na dakile ci gaba da yaduwarta.
A cewarsa: “Wannan kwamitin zai zama ja-gaba wajen jagorancin hukumomin gwamnati a jihar Bauchi kan barkewar Kwalara, tare da tsara dabarun kariya na dogon lokaci da suka yi daidai da Tsarin Ƙasa na Yaki da Cholera da kuma manufofin Cibiyar Dakile Cututtuka ta Najeriya (NCDC).”
Mataimakin gwamnan ya tunatar da mambobin kwamitocin cewa zaɓensu ya nuna ƙwarewarsu, sadaukarwarsu da muhimmancin rawar da za su taka wajen nasarar aikin, tare da fatan za su tabbatar da sa ido, gano cuta da wuri, da kuma ɗaukar matakin gaggawa idan ta barke.