Akalla dalibai 10 ne fargabar ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai a hanyarsu da zuwa zama Jarabawar shiga manyan makarantu, JAMB.
Ɗaliban suna cikin fasinjoji 18 da aka sace a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo, a yammacin Laraba, a Jihar Binuwai.
Wata majiya ta bayyan cewa ’yan bindigar sun tare motar ne da misalin karfe 8 na dare a kusa da Otukpo, suka kuma yi awon gaba da mafi yawan fasinjojin zuwa daji.
Majiyar ta ƙara da cewa mafi yawan waɗanda aka sace matasa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Otukpo domin rubuta jarabawar JAMB da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis.
“Direban motar da wani fasinja sun samu nasarar tserewa. Amma sauran matasa da suka nufi Otukpo domin zana jarrabawar JAMB an yi gaba da su,” in ji majiyar.
A nasa bangaren, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Benue, Ifeanyi Emenari, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace fasinjoji 14, yayin da mutum ɗaya ya tsere.
Ya kara da cewa shi da kansa ya isa Otukpo domin jagorantar aikin ceto wadanda aka yi garkuwa da sun.