Gwamnatin Najeriya ƙarkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na shan caccaka kan kama masu zanga-zangar tsadar rayuwa.
Bayyanar faifan bidiyon wasu matasa da a ganin ido basu haura shekara 15 zuwa 20 cikin mummuna yanayi da aka kama sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa ya janyo wa gwamnatin Tinubu tofin Allah ya tsine a kafafen sada zumunta.
Faifayin bidiyon da ya bayyana ya nuna yaran ne a gurfane a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
An gurfanar da yaran ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Obiora Egwuatu, ranar Juma’a.
Mai shari’a Egwuatu ya bayar da belin yaran su 72 akan Naira miliyan 10.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya kama yaran da ake zargi da laifin cin amanar ƙasa a lokacin da suke zanga-zangar tsadar rayuwa.
Sai dai wannan hukunci ya bar baya da ƙura domin jama’a na cigaba da bayyana yaran a matsayin waɗan da ba su kai ɗaukar hukunci ba.
Daga cikin waɗanda kawo yanzu suka ɓara dangane da wannan hukunci akwai ƙungiyar Amnesty International Mai Rajin Kare Haƙƙin Bil’adama.
Shima dai fitaccen malamin addinin Muslunci kuma tsohon Ministan Sadarwa Na Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami ya ɓara, inda ya rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa yana kira ga shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya ya yi bincike akan batun.
Kazalika Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa na jam’iyyar APC Mai wakiltar Neja ta Gabas ya bukaci Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, da Majalisar Shari’a ta kasa (NJC) su binciki yadda aka kama kananan yara kan zanga-zangar EndBadGovernance mai adawa da yunwa da tsadar rayuwa a Najeriya.