Shahararrun mahaddatan Alƙur’ani daga sassa daban-daban na duniya sun fara isa Pakistan domin halartar gasar karatun Alƙur’ani ta duniya.
Ma’aikatar Harkokin Addini ta Pakistan ce ke shirya gasar, wadda za a gudanar a birnin Islamabad daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Nuwamba, tare da halartar mahaddata daga ƙasashe 32 ciki har da Pakistan.
Mahaddata daga Kamaru da Togo da Mozambik da Uzbekistan sun isa Islamabad a daren Lahadi, yayin da mahalarta daga Jamus da Jordan da Aljeriya da Iraki da Libiya da Turkiyya suka isa ƙasar a ranar Litinin.
Haka kuma, mahaddata daga Tunisiya da Côte d’Ivoire da Masar da Tanzaniya da Gambiya da Najeriya da Qatar da Moroko da Faransa sun isa Islamabad domin shiga taron na kwanaki uku.
Fitaccen gwanin Alƙur’ani na duniya, Qari Syed Sadaqat Ali, ne zai kasance babban alƙalin gasar karatun Alƙur’anin ta ƙasa da ƙasa karo na biyu.
Ana sa ran sauran mahaddatan daga ƙasashen da za su halarta za su ci gaba da isa Pakistan har zuwa daren Litinin.