Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da ya auku ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Southern Ijaw da ke Jihar Bayelsa ya ƙaru zuwa mutum 29, yayin da sama da mutum 50 da suka tsira ke karɓar magani a asibitoci.
Gwamnan jihar, Douye Diri, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar jaje da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai masa.
Diri ya ce har yanzu ba za a iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu gaba ɗaya ba, domin ana ci gaba da ƙoƙarin ciro kwale-kwalen da ya haddasa hatsarin.
Sai dai ya ce akwai yiwuwar wasu fasinjoji na nan maƙale a cikin kwale-kwalen.
Gwamnan ya yi zargin cewa kwale-kwalen bai dace da zirga-zirgar ruwa ba, sannan kuma ya tashi ne daga wata tashar fasinjoji da ba a amince da ita ba.