Ina tsaka da yin aski aka ɗauke ruwa a Villa – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa ba talakawa ne kaɗai ke fuskantar matsaloli ba a ƙasar, har ma da shi kansa.

Amma kuma ya ce yana da yaƙinin cewa ƙasar za ta fita daga cikinsu nan ba da jimawa ba.

Yayin da yake jawabi a wurin taron addu’o’i da aka shirya masa a Legas, shugaban ƙasar ya ce matsalar ruwan sha ta kai har a fadarsa da ke Villa.

”A ranar Larabar makon da ya gabata ana tsaka da yi min aski a Villa kwai sai aka ɗauke ruwa, don haka muma muna fuskantar waɗannan matsaloli”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa ”ya kamata mu gyara waɗanann matsaloli na rashin wuta, rashin ruwa, rashin ayyukan ci gaba, kuma za mu gyara su ga Najeriya”, in ji shi.

Post masu alaƙa

INEC ta faɗi rumfunan da za ta yi gwajin zaɓen shugaban ƙasa

Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen Bayelsa ya kai 29

Ana shirin fara Gasar Karatun Qur’ani ta duniya a Pakistan