An yi kira ga kamfani dilancin labarai na Najeriya NAN da ya dawamar da fittacen dan kishin kasa kuma dan siyasa, marigayi Malam Aminu Kano(1920-1983).
Wani gogagen dan jarida kuma mai ba da shawara kan harkokin yada labarai a nan Kano, Alhaji Abdulkhadir Ahmad Ibrahim kwakwatawa ne ya yi wannan kira a cikin wata wasikar taya murna ga sabon manajan daraktan kamfanin dillancin labarai, Alhaji Ali Muhammad Ali.
Alhaji Abdulkhadir ya bayyana cewa ya zama wajibi NAN ta yi wani abu da zai sa a riƙa tunawa da marigayi malam Aminu Kano na har abada domin yaba wa marigayin kan gudunmowar da ya bayar wajen samar da Kanfanin shekaru kusan 63 da suka wuce.
Ya ce marigayin ya yi ta cel; ko ba komai, domin gayawa duniya halin da NajeriyaA ke ciki, dole ne a wancan lokaci ma’aikatar yada labarai ta bayyana tsare-tsaren kafa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ba dogara da na ƙasashen wajen ba.
Ibrahim ya ce, bayan shekaru 16 da wannan kira ne aka kafa kamfanin dillanci labarai na Neriyya ta hanyar doka ta19 na 1976 kuma ta fara aiki a ranar 2 ga oktoba 1978, tana ba da sabis na janar ga masu biyan kudi.
A ƙarshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba wa kanfanin dillancin labaran isasshen kuɗi domin samar da kayayyakin aiki wajen yaɗa labarai ga al’umma.