Ana taƙaddama kan zaɓen fitar da gwanin sanatan Zamfara ta Arewa

Wata sabuwar taƙaddama ta ɓarke a jihar siyasar jihar Zamfara kan zaɓen fitar da gwanin sanatan Zamfara ta Arewa a jam’iyyar APC.

A ranar Litinin ne jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fitar da gwani tsakanin ƴantakara uku, amma fafatwar ta fi zafi ne tsakanin sanata mai ci Sahabi Yau Kaura da wanda ke neman kujerar kuma tsohon Sanatan yankin, Sanata Tijjani Yahaya Kaura.

Sai dai bayan kammala zaɓen shugaban kwamitin zaɓen Dr Auwal Abdullahi Aliyu ya bayyana Sanata Sahabi Yau Kaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’a 49,176.

Yayin da Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya samu ƙuri’a 9,628.

To sai wani abu da ya ɗauki hankali shi ne jim kaɗan bayan shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanin ya bayyana wanda ya yi nasara, sai aka ga wasu ƴan kwamitinsa cikin wani bidiyo na bayyana Sanata Tijjani Yahaya a matsayin wanda ya yi nasara.

Lamarin da ya sa kowane ɓangare ke iƙirarin nasara a zaɓen.

Bayanai na cewa an gwabza zaɓen ne tsakanin magiya bayan manyan jiga-jigan siyasar jihar, Sanata Abdul’aziz Yari da ke goyon bayan Sanata Tijjani Yahaya, da kuma Ƙaramin Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Bello Matawalle da ke goyon bayan Sanata Sahabi.

Zuwa yanzu dai uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ba ta ce komai ba game da lamarin.

Post masu alaƙa

Kotu ta daure Saminu shekaru 15 kan kisan abokin kasuwancinsa, ta umarce shi da biyan Naira miliyan 10.

Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma’aikata Naira 70,000 alawus din sufuri

An fitar da matar da ta kai cutar Ebola Najeriya daga ƙasar