Yan sanda da ƙungiyoyi sun wayar da kan matasa kan gudanar da zaɓe cikin lumana a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar YOSPIS da gidauniyar AMG Foundation, sun gudanar da taron wayar da kan matasa da sauran al’umma kan muhimmancin gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana, ba tare da tashin hankali ba a faɗin jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce sun shirya zaman tattaunawar ne, a ci gaba da daukar matakan hukumomin tsaro ke ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaɓe.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa taron bai taƙaita ga matasa kaɗai ba, domin ya haɗa har da jami’an tsaro, inda suka tattauna tare da lalubo hanyoyin magance matsalolin da ka iya tasowa a ranar zaɓe.
A nasa jawabin, shugaban gidauniyar AMG Foundation, Dakta Aminu Garba Magashi, ya bayyana cewa shekaru huɗu da suka gabata, sun taɓa gudanar da irin wannan zama domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin matasa da jami’an tsaro, don ganin an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.Taron tattaunawar ya samu halartar matasa, ƙungiyoyin fararen hula, ’yan jarida, masu amfani da shafukan sada zumunta, lauyoyi da jami’an tsaro.

An kuma tattauna ƙalubalen da ake fuskanta yayin gudanar da zaɓe, tare da lalubo hanyoyin magance su domin tabbatar da zaɓe cikin lumana da kwanciyar hankali a jihar Kano.

 

Post masu alaƙa

Kotu ta yankewa Mustapha Usha hukuncin kisa kan kashe matashi a unguwar Bambazau

Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da yin barazanar garkuwa da Dagacin garin Bangare a Kano.

INEC ta sanya ranar nazari kan korafe-korafe Pantami, Aminu Abdussalam da saura ya takara