Ana zargin wasu batagarin mutane sun shiga gidan wata matar aure mai suna, Alawiya Nasiru yar shekaru 24 , inda suka yi mata kisan gilla tare da danta mai suna, Ibrahim Khalil ,mai shekaru uku, a unguwar Sabuwar Gandu dake karamar hukumar Kumbotso.
Lamarin ya faru ne a ranar juma’a , inda ake zargin sun yi amfani da makami kafin su halaka su ta hanyar kunna musu wuta.
Koda a watan Nuwambar da ya gabata sai da wasu batagari suka halaka wasu matan aure biyu ,Hauwa’u Yakubu da Zahra’u Aliyu, wadanda dukkansu mata ne ga, Alhaji Ashiru Shu’aibu Usaini, sannan suka kunna wa gidan wuta, a unguwar Tudun Yola Kano.
Yankin na Sabuwar Gandu,Yasha fama da irin wadannan matsaloli domin, an taba tsintar gawar wata yarinya a cikin wani Kango bayan an cire mata wasu sassan jikinta da gawar wani jariri da aka jefar.
Kisan matar auren da kuma danta, ya kara sanya al’ummar Sabuwar Gandun cikin zulimi da firgici, inda suka ce wannan tsantsar rashin Imani ne.
- Tsohon shugaban hukumar shigi da fici Muhammad Babandede OFR, OCM, ya buƙaci ma’aurata su dinga haƙuri da juna.
- Kotu Ta Sa Ranar Yanke Hukunci A Shari’ar Abba Kyari Da NDLEA
Mijin marigayiyar, Nasiru Usaini, ya bayyana cewa, ya fita ya barsu lafiya amma lokacin da ya dawo sai ya tarar an sassare su sannan aka kunna musu wuta,wanda hakan ne yayi sanadiyar rasuwarsu.
Hajara ƙanwa ce ga Nasiru Usaini, ta bayyana cewa sun tsinci labarin ne kawai kuma ya tayar musu da hankalin bisa rashin imanin da aka yiwa matar yayanta da kuma ɗanta.
A safiyar asabar din nan aka yi janazar mamatan, sannan aka binne su bisa koyarwar addinin musulinci.
Jama’a na fatan mahukunta za su kara fadada bincike don gano me ke sanya batagari, ɓullowa da sabon salon yiwa matan aure kisan gilla tare da kunna mu su wuta.
ga rahotan Mujahid Wada Musa