Ana zargin mahaifi da kashe ’yarsa kan auren dole a Katsina

Wani magidanci ya shiga hannun hukuma kan zargin kashe ’yarsa a sakamakon yi mata duka saboda ta ƙi amincewa da auren dole a Jihar Kastina.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce ta fara bincike kan mutuwar matashiyar mai suna Ummul Khair, wadda ake zargin ta rasu bayan nata mahaifinta ya yi mata duka saboda ƙin amincewa ta auri wani mutum da ya zaɓa mata.

Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, ’yan sanda daga caji ofis na Babbar Kasuwar Katsina suka kama magidancin mai suna Kabir Sani, wanda direban motar haya ne kuma mazaunin unguwar Shagari Low-Cost da ke cikin birnin Katsina.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilanmu cewa marigayiyar, wadda aka kiyasta shekarunta tsakanin 16 zuwa 18, ta daɗe tana adawa da yunƙurin mahaifinta na aurar da ita ga mutumin da ya zaɓa mata, lamarin da suka ce ya janyo saɓanin a cikin iyalinsu.

A cewar shaidu, ana zargin mahaifin ya fara dukan ta tun ranar Laraba. Maƙwabta sun ce sun ji kukanta, kuma sun yi ta buga ƙofar gidan domin su shiga su ƙwace ta, amma mahaifin ya ki buɗe musu ƙofa.

Rahotanni sun ce dukan ya ci gaba har zuwa safiyar Alhamis, inda daga bisani yarinyar ta suma.

An gano faruwar lamarin ne lokacin da wasu ƙawayen marigayiyar suka je gidansu a safiyar Alhamis domin su tafi makaranta tare.

A cewar rahotanni, sun tarar da ita babu rai, yayin da mahaifinta ke shirya jana’izarta, lamarin da ya sa suka sanar da maƙwabta, waɗanda daga bisani suka kai rahoto ga ’yan sanda.

Wani mazaunin unguwar ya ce, “Mun ji tana kuka tsawon dare, kuma mun yi ƙoƙarin shiga domin ceto ta, amma mahaifinta ya ƙi buɗe mana kofa. Da safe muka ji cewa ta rasu. Lamarin ya girgiza ɗaukacin mutanen unguwar.”

Wani mazaunin yankin ya ce marigayiyar ta dage cewa ita ce za ta yanke shawarar wanda za ta aura, yayin da mahaifinta ya nace sai ta auri mutumin da ya zaɓa mata.

An yi jana’izar marigayiyar a safiyar Alhamis, tare da binne ta a maƙabartar Abbatuwa da ke birnin Katsina, bisa koyarwar addinin Musulunci.

Majiyoyin ’yan sanda sun tabbatar da cewa wanda ake zargin na ci gaba da kasancewa a tsare a ofishin ’yan sanda na Babbar Kasuwar Katsina, yayin da jami’an bincike ke ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar yarinyar.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya ce yana da masaniya kan lamarin, amma zai yi ƙarin bayani ne bayan kammala binciken da ake yi.

Post masu alaƙa

An kama mutum 2 kan zargin sayar da filayen gwamnatin a Kano

Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos

Yan sanda sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙwato dabbobi 76 a Katsina