Jigawa ta amince da rancen naira biliyan 3.5 domin tabbatar da kujerun aikin Hajjin 2027

Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen Naira miliyan dubu uku, da miliyan dari biyar ga Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar domin tabbatar da kujerun aikin Hajjin shekarar 2027, da kuma sauƙaƙa shirye-shiryen gudanar da aikin ga alhazan jihar.

An bayyana cewa an amince da rancen ne domin bai wa masu niyyar zuwa aikin Hajji damar biyan kuɗin ajiye kujerunsu cikin wa’adin da Hukumar Hajji ta ƙasar Saudiyya ta gindaya.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Habibu Yusuf Babura, ANIPR, ya fitar.

Sanarwar ta ce matakin ya nuna ƙudirin Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, na ci gaba da tallafa wa harkokin addini da kuma sauƙaƙa wa al’ummar jihar cika ɗaya daga cikin rukunan Musulunci.

Post masu alaƙa

NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun Hajjin 2027

Gwamnati ta sa dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga a Neja

Sai ’yan Najeriya sun sayi litar man fetur N5,000 idan Tinubu ya zarce