ASUU ta nemi gwamnati ta biya malaman jami’o’i albashin da aka riƙesu

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta sake buƙatar gwamnatin tarayya ta biya albashin da aka riƙe wa malamai tare da warware sauran matsalolin jin daɗin ma’aikatan jami’o’i.

Shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Jami’ar Jos, inda ya ce gwamnati ta cika sauran sharuddan yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar a watan Disamban 2025 domin dawo da zaman lafiya a jami’o’in gwamnati.

Ya ce warware waɗannan matsaloli zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar malamai da ba su damar mayar da hankali kan koyarwa, bincike da hidimtawa al’umma.

ASUU ta kuma yi kira ga gwamnati ta ba ilimi muhimmanci, ta inganta kuɗaɗen da ake warewa jami’o’i, da kuma samar da manufofin tattalin arziki da za su rage talauci da samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.

Post masu alaƙa

Pantami ya lashe zaben fid da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe

Zaɓen 2027: CP Bakori ya gargaɗi jami’an ’yan sanda kan tsoma baki a siyasa.

Kamfanin Tianneng ya ƙaddamar da sabbin babura masu kafa biyu da masu kafa uku, waɗanda ke amfani da wutar lantarki, a wani biki da ya gudana a nan Kano.