Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya Sulaiman Abba ya fice daga jam’iyar APC.

Tohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Suleiman Abba, ya fice daga Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa.
Abba ya sanar da sauya sheƙarsa ne a ranar Asabar yayin wani gangami da aka gudanar a garin Bamaina, mahaifar wani jigo na PDP kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, inda shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta suka tarbe shi.
‎
‎Tsohon shugaban ‘yan sandan ya ce ya shiga jam’iyyar PDP ne domin cika burinsa na tsayawa takarar wakilcin Mazabar Sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma a Majalisar Dokoki ta Ƙasa

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun gaiyaci Aminu Warkal kan zargin nuna bindiga.

2027: Sama da mutum 10,000 sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da Namadi a mazabar Limawa

Gwamnonin Arewa maso Gabas na yin taro a Maiduguri