Gwamnati ta maka El-Rufai a Kotu
Gwamnatin Tarayya ta maka Nasir El-Rufai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a kotu, kan zargin kutsen intanet a layin sadarwar Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu. Hukumar Tsaro ta DSS ce ta shigar da kara gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda take tuhumar El-Rufai da laifuka uku masu alaka da kutsen intanet. […]