Yadda Aka Karrama Janar Murtala Muhammed A Abuja

Manyan mutane sun hallara a Abuja, a ranar Juma’a, domin tunawa da cika shekaru 50 da kisan tsohon Shugaban ƙasa, Janar Murtala Muhammed.

An kashe marigayi Janar ne tare da wasu muƙarrabansa, a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Legas, ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

Jami’an rundunar sojin Najeriya sun yi bikin karrama shi tare da wasu manyan baƙi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Farfesa Ibrahim Gambari, fitaccen jami’in diflomasiyya kuma tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.