Hukumar EFCC Ta Kama Ifeanyi Okowa Kan Karkatar Da Tiriliyan 1.3
Jami’an EFCC sun kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da naira biliyan dubu daya da biliyan dari uku wato tiriliyan 1.3.
Jami’an EFCC sun kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da naira biliyan dubu daya da biliyan dari uku wato tiriliyan 1.3.
Lamari na ƙara rincaɓewa a jam’iyya mai mulki a Kano NNPP, inda wasu majiyoyi suka tabbatar da cewa gwaman Abba ya daina ɗaga kiran mai gidansa Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Taron Editocin Najeriya na shekara shekara ANEC, a bana wanda shine karo na 20 zai gudana ne a Yenagoa, Babban Birnin Jihar Bayelsa.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya naɗa Farfesa Isa Ali Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniya.
Ɗan Majalisa mai wakiltar Dala a tsakiyar birnin Kano kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, Ali Sani Madakin Gini ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin jam’iyyarsa ta NNPP.
Gwamnatin Najeriya ƙarkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na shan caccaka kan kama masu zanga-zangar tsadar rayuwa. Bayyanar faifan bidiyon wasu matasa da a ganin ido basu haura shekara 15 zuwa 20 cikin mummuna yanayi da aka kama sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa ya janyo wa gwamnatin Tinubu tofin Allah ya tsine a kafafen sada zumunta. Faifayin […]
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye ƙudirinsa na ƙara haraji.
Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin ɗaukar nauyin wanke ƙodar duk wani ɗan jihar da ke ɗauke da ciwon ƙodar da ke buƙatar wankewa. Wannan ya zo ne a cikin wani bayani da Kwamishinan Lafiya na jihar Jigawa Dokta Abdullahi Muhammad Kainuwa ya yi wa abokin aikinmu Hassan Abdu Mai Bulawus, a yayin wani taro da […]
Tun bayan faruwar ambaliyar ruwa da tayi sanadiyar rasuwar mutane aƙalla 95 tare da raba wasu da muhallan su, ana cigaba da aikin ceto a garin Valeancia dake ƙasar Sifaniya.
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alƙawarin taimakawa masana masu bincike akan ciwon ƙoda da ke addabar jama’ar wasu yankuna a jihar.