Hukumar EFCC Ta Kama Ifeanyi Okowa Kan Karkatar Da Tiriliyan 1.3

Jami’an EFCC sun kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da naira biliyan dubu daya da biliyan dari uku wato tiriliyan 1.3.

Mai magana da yawun hukumar ne ya tabbatar da kama Mista Okowa domin gudanar da bincike.

Okowa ne ya yi wa ɗan takarar shugabancin ƙasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar mataimaki a zaɓen da ya gabata na shekarar 2023.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa