Hukumar hana cin hanci da rashawa ta ICPC ta wanke fadar shugaban kasa daga duk wani zargi na nadin darektan janar na hukumar nan ta Bogi Adeniyi Adeyemi da kum kafa ita kanta wannan hukuma.
Hukumar ta bayyana cewa takardar dashi Adeyemi ya gabatar ta nadashi a wannan mukami ta bogi ce kuma ba daga fadar shugaban kasa aka bashi takardar ba.
Shugaban hukumar ta ICPC Musa Adamu ne ya sanar da hakan yayinda yake mika rahoton wucin gadi na binciken da hukumar keyi kan wannan badakala ga shugaban kasa Bola ahmad Tinubu.
Ya bayyana cewa binciken da hukumar tayi ya nuna cewa fadar shugaban kasa bata da laifi ko kadan inda yace duk wasu takardu da hukumar ta bogi ke amfani dasu basu fito daga fadar ba.
Musa adamu ya sanar da cewa naci gaba da bincike dan gano yadda aka haihu a ragaya.