Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (Immigration) ta ce sabon tsarin da ta bullo da shi na mayar da buga fasfo a Abuja bai shafi karɓa ko yin rijistar fasfo a jihohi ba.
Hukumar ta ce rahotannin da ke cewa za a ɗauke cibiyoyin gudanar da fasfo daga Kano ba gaskiya ba ne, kuma mutane sun yi kuskuren fahimtar abin da ake nufi.
Bayanin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da cece-ku-ce kan wata takarda da ta nuna cewa an mayar da wasu cibiyoyin buga fasfo daga wasu jihohin zuwa Abuja kaɗai.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a jihar Kano, DSI Muhammad Auwal, ya shaida wa BBC cewa sabon tsarin ya fara aiki tun farkon shekarar nan, kuma an aiwatar da shi a wasu jihohin a rukuni-rukuni.
“Ba wai za a daina rijistar fasfo ko kuma karɓarsa a jihohi ba ne. Buga fasfo ne aka mayar zuwa Abuja,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, an fara aiwatar da tsarin ne a jihohin Nasarawa, Kogi, Borno da Yobe, kuma za a ci gaba da faɗaɗa shi zuwa sauran jihohi.
DSI Auwal ya tabbatar wa BBC cewa takardar da ake ta yaɗawa daga hukumar ta fito, amma ya ce takarda ce ta cikin gida wadda ba a yi niyyar ta fito bainar jama’a ba.
Ya ce manufar mayar da buga fasfo wuri guda ita ce ƙarfafa tsarin tsaro da kuma rage yiwuwar buga fasfo na bogi.
Dangane da rashin ganin Legas cikin jerin jihohin da sauyin ya shafa, ya ce “ita ma tana cikin rukuni na biyar,” kuma za a aiwatar da sabon tsarin a can nan ba da jimawa ba.