Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya buƙaci sabbin jami’an rundunar da su kasance masu ladabi, biyayya ga doka da oda, gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da lacca ga ɗaliban jami’an ’yan sanda masu muƙamin Mataimakan Sufeto, ajin ASP Course 8, a kwalejin horar da yan sandan Najeriya da ke Wudil.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya fitar da sanarwar, a ranar Alhamis.
A yayin laccar, CP Bakori ya bayyana cewa aikin ’yan sanda a wannan zamani ba ya dogara da amfani da ƙarfi kaɗai, sai dai yana buƙatar ƙwarewa, amfani da fasaha, mutunta haƙƙin bil’adama da kyakkyawar mu’amala da al’umma.
Ya kuma ba jami’an shawarar su kiyaye mutuncinsu, su kasance masu bin umarnin da doka ta amince da su, tare da guje wa amfani da muƙamansu ta hanyar da za ta tauye haƙƙin jama’a.
Kwamishinan, wanda ya shafe shekaru 30 yana aikin ’yan sanda, ya bayyana cewa ladabi da gaskiya su ne ginshiƙan jagoranci nagari da kuma samun amincewar al’umma.
Ya kuma yi bayani kan dabarun inganta tsaro a Kano, ciki har da amfani da bayanan sirri, haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran hukumomin tsaro, tare da Operation Kukan Kura da rundunar ke gudanarwa domin yaƙi da ’yan daba da sauran laifuffuka.
CP Bakori ya yabawa al’ummar Kano bisa goyon baya, addu’o’i da haɗin gwiwar da suke bai wa rundunar, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen inganta tsaro a jihar.
A ƙarshe, ya buƙaci jami’an da su ci gaba da neman ilimi da ƙwarewa, tare da ba manyansu shawarwari na gaskiya da ƙwarewa.
Ya jaddada cewa samun muƙami abu ne da ake ba mutum, amma samun girmamawa da amincewar jama’a na buƙatar aiki tuƙuru, gaskiya da kyawawan ɗabi’u.
