Home » Wakilan Arewa A Zauren Majalisa Sun Nuna Damuwarsu Kan Dokar Haraji

Wakilan Arewa A Zauren Majalisa Sun Nuna Damuwarsu Kan Dokar Haraji

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Majalisar Wakilai

Yan Majalisar Wakilai da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna damuwarsu kan wasu kudurori hudu da zasu  sake fasalin dokar harajin Najeriya. 

A halin yanzu dai wannan kuduri da zai yi ba da damar aiwatar da wannan sabuwar doka na gaban majalisar suna nazari a kanta.

‘Yan Majalisar sun yi wannan jawabi ne a zaman tattaunawa da majalisar ta yi da mambobin kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji a ranar Litinin.

Kudurorin gyaran da ake shirin yi wa rabon haraji (VAT), da suka haifar da cece-kuce su ne: 

  1. Dokar Harajin ta 2024, wadda ake sa ran za ta samar da tsarin kasafin kudin haraji a kasar.
  2. Dokar Kula da Haraji, wadda za ta samar da tsayayyen tsari na doka game da duk harajin da ke cikin kasa tare da rage rikice-rikice.
  3. Dokar Kafa Haraji , wadda za ta soke dokar Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma kafa Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Najeriya (NRS). sai kuma 
  4. Dokar kafa hukumar tattara haraji ta hadin gwiwa, wadda za ta samar da kotun sasanta rikicin haraji.

Tun a baya dai Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da kungiyar  gwamnonin sun bukaci shugaba Tinubu ya janye kudirin don ci gaba da tuntubar juna.

Haka zalika, shugabannin Arewa da suka hada da sarakunan gargajiya da ’yan majalisar dokoki, sun nuna rashin amincewarsu, inda suka yi zargin garambawul din da ake shirin yi, ya fi karkata wurin cutar da yankin.

Sai dai duk da wannan nuna rashin amincewa da wannan kuduri,  Tinubu ya ce ya kamata ta ci gaba da aiki a kai, yana mai jaddada cewa tattaunawar da ake yi tana ba da damar yin amfani da bayanai da gyara ba tare da an janye kudirin ba.

A zaman da aka yi a ranar Litinin, ’yan majalisar da suka fito daga Arewa da suka hada da Honorabul Yusuf Adamu Gagdi da Ahmed Jaha Babawo da Zainab Gimba da kuma Zakariah Dauda Nyampah sun bayyana damuwarsu game da illar da kudurorin za su yi wa yankin.

Sun yi iƙikrarin cewa tattalin arzikin yankin, wanda ya riga ya raunana a sakamakon matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi, na iya kara lalacewa karkashin dokar da ake shirin yi.

Sai dai tawagar fadar shugaban kasa na sake tsarin harajin ya kawar da fargabar, inda ta ce rabon kudin harajin na yanzu ya fifita wasu jihohi ’yan kadan, kuma hakan rashin adalci ne ga wasu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?