Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal ya yi murabus daga jam’iyyar ADC ta haɗakar ‘yan adawa.
Kafofin labarai a Najeriya sun ambato Babachir na bayyana fita daga ADC a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan Litinin 1 ga Yulin 2026.
Tsohon Sakataren Gwamnatin ya yi zargin cewa kurakurai sun ɓata zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar kuma an jirkita sakamakon zaɓen don ya fifita ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC Atiku Abubakar da mutanen da suke goyon bayansa.
Ya ce yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwanin ya nakasa ƙwarin gwiwar da ake da shi a tsarin dimokraɗiyyar cikin gida na jam’iyyar sannan ya yi tasiri ga shawararsa ta barin ADC.
Babachir ya ce ba zai iya ci gaba da zama a jam’iyyar da in ji shi aka mayar da halastattun ‘yan siyasan da suka yi nasara ba sannan aka maye gurbinsu da wasu shafaffu da mai.
Zuwa yanzu shugabancin ADC da Atiku Abubakar ba su ce uffan a bainar jama’a kan batun fitar Babachir Lawal daga jam’iyyar ba, haka kuma ba a ji martaninsu a kan zarge-zargen da ya yi ba.