DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja

Hukumar Tsaron farin kaya (DSS) ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu a wata ƙungiyar da ke safarar makamai ga ’yan bindiga da suka kai harin sace ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Papiri, a Jihar Neja.
‎Daga cikin waɗanda aka kama har da wasu ’yan ƙasar waje biyu daga Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke nuna cewa akwai haɗin gwiwa tsakanin ’yan cikin gida da na waje wurin aikata laifin.
‎Rahotanni sun bayyana cewa binciken sirri ne ya kai ga kama waɗanda ake zargin, tare da gano makamai da harsasai da ake kyautata zaton za a kai wa masu kai hare-hare.
‎Har yanzu DSS ba ta fitar da cikakken bayani na hukuma ba, amma majiyoyin tsaro sun ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na wargaza hanyoyin da ake amfani da su wajen samar wa ’yan bindiga makamai a Najeriya

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.