Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da rasuwar Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.
Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya zama shugaban rundunar Sojin Kasa Najeriya a ranar 19 ga watan Yuni, 2023.
An tabbatar da rasuwar Janar Taoreed a ranar Talata bayan rashin lafiyar da ta tilasta fitar da dashi waje tun a kwanakin baya.
- Hukumar EFCC Ta Kama Ifeanyi Okowa Kan Karkatar Da Tiriliyan 1.3
- Za A Yi Taron Editocin Bana A Bayelsa
Allah Ya yi wa Janar Lagbaja rasuwa ne yana da shekaru 56, ya bar matarsa Mariya, da ’ya’ya biyu.
Hadimin Shugaban Kasa Kan Yada Labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana rasuwar Babban Hafsan Sojin yana mai mika ta’aziyyar Shugaba Bola Tinubu game da babban rashin da Najeriya ta yi.