• Home  
  • Za A Yi Taron Editocin Bana A Bayelsa 
- Babban Labari - Labarai

Za A Yi Taron Editocin Bana A Bayelsa 

Taron Editocin Najeriya na shekara shekara ANEC, a bana wanda shine karo na 20 zai gudana ne a Yenagoa, Babban Birnin Jihar Bayelsa.

Taron Editocin Najeriya na shekara shekara ANEC, a bana wanda shine karo na 20 zai gudana ne a Yenagoa, Babban Birnin Jihar Bayelsa.

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Gwamna Douye Diri na Jihar Bayelsa, da Ministan Kasafin da Tsare tsaren Tattalin Arziki, Atiku Abubakar Bagudu da Ministan Yada Labarai da Wayar da kan al’umma, Mohammed Idris da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da mashahuran ‘yan kasuwa ne za su jagoranci tattaunawa akan tattalin arziki da tsaro daga cikim taken taron.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Editocin Najeria NGE, Eze Anaba da Sakatare Iyabosa Uwugiaren yace, Babban Edita da kwararre kuma shugaban Thisday da Arise, Prince Nduka Obaigbena shi zai jagoranci tarom.

Tsaohon Gwamnan Jihar Ogun Aremu Shegun Osoba da Mawallafi kuma shugaban Jaridar Vanguard Chief Sam Amuka da sauran masana a harkokin yada labarai zasu gabatarda kasidu akan dabarun samar da kudade ga kafafen yada labarai da kuma dabarun magance kalubalen wajen amfani da manhajar AI da sauran batutuwa masu tasowa a bangaren aikin jarida.

Sanarwar da aka aike dakin labarai na gida Radio da Talabijin na Muhasa ya kara da cewa Cibiyoyi masu zaman kansu dana cigaban al’umma suna daga cikin wadanda zasu gabatar da kasidu a taron na shekara shekara na NGE daga ranar 7 zuwa 9 ga wannan watan na Nuwamba.

A tarihi taron ANEC a wannan shekara zai samu halarta editoci sama da 350 daga fadin kasar nan tun daga locacin da wannan gwamnati ta hau mulki.

Kungiyar ta bayyana cewa tun daga hawau gwamnati mai mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023 ‘ya’yan kungiyar sun sha tafka muhawara inda hankali ya karkata tare da neman sauye sauye don sake gina ingantaccen tattalin arzikin kasar mai inganci da zai samar da kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa.

A cewar editocin sauye sauyen da gwamnatin tayi daga hawar ta ya haifar da matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya jefa rayuwar al’umma cikin mayuyacin hali.

Tace domin shawo kan matsalolin gwamnati tayi ta aiwatar da tallafin kudi domin kaiwa gidaje sama da miliyan 15 da tsaurara matakan hada hadan kudade sannan babban bankin Najeriya na kokarin tabbatar da daidaiton farashin kudade.

Taken taro na bana “hanyar ci gaban tattalin Arziki da dabarun ci gaban albarkatun kas” yayi daida da bayanan kiyasin talauci da ya kai kaso 40 cikin 100 da ‘yan Najeriya miliyan 88 dake fama da talauci.

Dangane da dorewar Kafafen yada labarai, kungiyar kwararrun editocin ta bayyana matsaya mai karfi a kan harkar, sun kuma fito da hanyoyi kwarara na tallafawa kafafen yada labarai.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa zata mai da hankali wajen zakulo dabaru da manufofin magance kalubalen tattalin arzikin kasa da bunkasa kafafen yada labarai.

Taro wanda aka fara shi a shekarar 2004 zai kuma kaddamar da sababbin ‘ya’yan kungiyar,editoci 12.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000