• Home  
  • Hukumar EFCC Ta Kama Ifeanyi Okowa Kan Karkatar Da Tiriliyan 1.3
- Babban Labari - Labarai

Hukumar EFCC Ta Kama Ifeanyi Okowa Kan Karkatar Da Tiriliyan 1.3

Jami’an EFCC sun kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da naira biliyan dubu daya da biliyan dari uku wato tiriliyan 1.3.

Jami’an EFCC sun kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa bisa zargin karkatar da naira biliyan dubu daya da biliyan dari uku wato tiriliyan 1.3.

Naira Tiriliyan 1.3 da aka ruwaito na wakiltar kashi 13% na asusun rarar kudi daga asusun tarayya na jihar Delta tsakanin 2015 zuwa 2023.

Mai magana da yawun hukumar ne ya tabbatar da kama Mista Okowa domin gudanar da bincike.

Okowa ne ya yi wa ɗan takarar shugabancin ƙasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar mataimaki a zaɓen da ya gabata na shekarar 2023.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000