Babban Layin Wutar Lantarkin Da Ke Kawo Wuta Arewa Ya Sake Ɗaukewa

A jiya Litinin ne babban layin dake samar da wuta ga Jihohin Arewacin Najeriya na sake ɗaukewa.

Bayanin sake ɗaukewar layin wutar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babbar Manajan Hulɗa da Jama’a ta Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya, Ndidi Mbah ta fitar a safiyar Talata.

A cikin makonni biyu, wannan shine karo na shida da babban layin wutar ke lalacewa .

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukacin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na cikin duhu, da kuma wani yankin na Arewa ta Tsakiya. Mbah ta sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, inda har yanzu ake gudanar da binciken inda matsalar take.

A makonnin baya dai matsalar ɗaukewar wutar lantarki yana neman zama ruwan dare a Najeriya. Cikin watanni biyu, wannan shine karo na shida da babban layin raba hasken wutar lantarkin yana ɗaukewa.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.