Home » Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Rugurguza Kaswuanci A Arewacin Najeriya

Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Rugurguza Kaswuanci A Arewacin Najeriya

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Tun bayan ɗaukewar babban layin wutar lantarkin da yake samar wa da Arewacin Najeriya wutar lantarki, iyalai da masana’antu a yankin suka shiga  matsaloli saboda rashin hasken wutar.

An sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suka ƙarfin 330kv da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, inda har yanzu ake gudanar da binciken inda matsalar take.

Kimanin kwanaki goma kenan tun bayan ɗaukewar wutar. Wannan matsala ta faru ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa, inda ake kokawa kan tashin gwauron zabi na kayan masarufi a Najeriya.

Wannan ne ya sa ƙanana da matsakaitan yan kasuwa suka rufe guraren sana’o’in su, yayin da wasu suke kai wa da ƙyar.

Kamfanonin da suke fuskantar wannan matsala sun haɗar da Kamfanonin casar shinkafa da na man gyaɗa da kamfanonin samar da ruwa na leda da teloli da masu markaɗe da masu sana’ar aski da walda duk sun nu na takaicin su kan yadda matsalar rashin wutar ke shafar sana’o’in su.

Daga ranar 4 ga watan Fabrairu ne zuwa yanzu, sau bakwai aka samu lalacewar babban layin wutar lantarki a kasar, mai yawan al’umma sama da miliyan 220.

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Nijeriya (TCN) ya ce, duk da haka, kawo yanzu sau ɗaya ne wutar ta ɗauke gaba ɗaya a fadin ƙasar a bana.

Abun tambayar anan idan wannan matsala ta cigaba menene makomar masu aiki da wutar, musamman masu sana’o’i?

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?