Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan.
Farfesa ya bayyana hakan ne a ranar Asabar cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mista Rotimi Oyekanmi, ya fitar.
A baya, an samu rahotanni a kafafen sada zumunta wanda suka nuna cewa Farfesa Yakubu ya rasu bayan jinya a wani asibiti da ke Landan.
Sanarwar ta bayyana cewa labarin ba gaskiya ba ne.
“Mun samu labarin wata jita-jitar ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya rasu a wani asibiti da ke Landan.
“An fara yaɗa wannan jita-jitar tun a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba, 2024.
“Muna kiran jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar.“Farfesa Yakubu yana nan cikin ƙoshin lafiya, kuma bai je Landan cikin shekaru biyu da suka wuce ba,” in ji sanarwar.
- Sojoji Sun Ragargaji Sansanonin Lakurawa
- Ba Sulhu Tsakaninmu Da ECOWAS – Nijar, Mali da Burkina Faso
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Yakubu ya halarci wasu taruka da suka shafi INEC, ciki har da ganawa da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Zaɓe a ranar Laraba.
Sanarwar ta ƙara da cewar ya halarci wani taro da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba, 2024.
Sanarwar ta ce an taɓa yaɗa irin wannan ƙaryar a baya, inda aka ce shugaban hukumar ya rasu.
“Yanzu kuma, bayan shekaru uku, sun sake yaɗa irin wannan ƙaryar da suka yi a baya,” in ji sanarwar.
Hukumar ta buƙaci jama’a su fahimci illar da irin waɗannan jita-jitar ke haifarwa ga mutum da al’umma baki ɗaya.
Ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da aiki tare da kafafen yaɗa labarai na gaskiya domin yaƙi da labaran ƙarya.