Home » Ba Sulhu Tsakaninmu Da ECOWAS – Nijar, Mali da Burkina Faso

Ba Sulhu Tsakaninmu Da ECOWAS – Nijar, Mali da Burkina Faso

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Shugabannin Ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, sun sake tabbatar da matsayarsu na ficewa daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS).

Shugabannin sun bayyana wannan matsaya ne yayin wani taro da ministocin harkokin wajen da suka gudanar a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, a ranar Juma’a.

Taron, ya mayar da hankali kan samar da hanyoyin da za su bai wa jama’arsu damar yin zirga-zirga tare da samun damar gudanar da kasuwanci cikin sauƙi a faɗin yankin.

Ministocin sun bayyana aniyarsu na kafa kwamitin ƙwararru da zai nazarci hanyoyin da za su tabbatar da cewa ficewar ƙasashen bai kawo wa jama’arsu matsala a harkokin yau da kullum ba.

Fitar ƙasashen uku daga ECOWAS ta samo asali ne daga taƙaddamar da ta kunno kai bayan juyin mulki.

ECOWAS, ta sanya wa ƙasashen takunkumi, ciki har da kulle iyakokinsu da hana su zirga-zirga da kasuwanci, da nufin dawo da su ta ƙarfi.

Mali, Nijar da Burkina Faso sun yi Allah-wadai da matakin, inda suka yi zargin takunkumin ya ƙara ta’azzara wahalar rayuwa ga al’ummarsu.

A watan Agustan 2023, ƙasashen uku sun ƙulla sabon ƙawance domin ƙarfafa haɗin kai, tsaro, da kuma kare muradunsu a yankin Sahel.

Ƙawancen ya maye musu gurbin ECOWAS, ya kuma mayar da hankali kan tsaron iyakokinsu da kare yankunansu daga barazanar ta’addanci.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?