A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne rundunar sojin Najeriya ta yi wa manyan hafsoshinta 656 ritaya, wadanda suka shafe shekaru 35 a suna aiki.
An gudanar da bikin ritayar ne a cibiyar horas da sojoji rayuwar fararen hula da ke Oshodi jihar Legas, bayan sun kwashe watanni shida ana basu horo na musamman domin tunkarar rayuwar farar hula.
Wadanda suka yi ritaya sun hada da sojojin ƙasa 535 na sama 86 sai kuma na ruwa guda 35.
Babban hafsan sojin saman Najeriya Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya jinjinawa wadanda suka yi ritaya, inda ya yaba da irin gudunmawar da suka bayar wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
Ya ce“Wannan horon ya samar muku da ilimi da dabarun da ake bukata don sauya rayuwa daga ta soji zuwa farar hula.
“Kun samu horo na musamman na zama manajoji, ’yan kasuwa, masu bayar da gudummawa ga ci gaban kasa,”
Babban hafsan sojin saman Najeriya ya bai wa waɗanda suka yi ritaya shawarar su rungumi sabuwar rayuwar farar hula da ƙwarin gwiwa, ya tunatar da su cewa horon da suka samu da gogewar da suka yi zai tabbatar da samun nasarar rayuwar su ta farar hula.
Kwamandan na NAFRC, Air Vice Marshal Mamman, ya bayyana irin rawar da cibiyarsa ke takawa wurin tarbiyyar jami’an da suka yi ritaya.
Ya ce “NAFRC ta horar da jami’an soji sama da dubu 51, tare da samar musu da dabarun dogaro da kai bayan ritaya.
Mamman ya buƙaci wadanda suka yi ritaya da su kyautata niyyar su.
Ya ce, “Kada ku ji tsoron gaba. Horo da dabarun da kuka samu, zai taimaka muku wurin cin nasara a rayuwa”