Dakarun Rundunar Sojin Najeriya ta ‘Operation Fansan Yamma’ sun tarwatsa sansanoni 22 na ‘yan ta’addan Lakurawa a jihar Sakkwato.
Hakazalika sojojin sun yi nasarar kashe wasu da dama kuma sun kwato makamai da alburusai.
Mukaddashin babban kwamandan runduna ta 8 kuma kwamandan sashi na 2 na rundunar Fansar Yamma, Birgediya Janar Ibikunle Ajose ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake jawabi ga runduna ta musamman da aka tura domin murkushe Lakurawa a jihohin Sakkwato da Kebbi a ranar Juma’a.
- Ba Sulhu Tsakaninmu Da ECOWAS – Nijar, Mali da Burkina Faso
- Kaso 40 Na Masu Mutuwa Da Cutar Malariya A Duniya ‘Yan Najeriya Ne _WHO
Ya ce, idan aka tura wasu rundunar ta musamman, to babu shakka zai kara wa rundunar da ke aiki a yankin ƙwarin gwiwa da kuzari wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma baki daya.