Bankin Duniya Ya Sanya Nera Cikin Jerin Kuɗaɗen Daba Su Da Daraja A Afrika.

A cikin wani rahoto da bankin duniyar ya fitar, Naira da ƙasar Najeriya ke amfani da ita na ɗaya daga cikin takardun kuɗi marasa daraja a Afirka ta yamma a shekarar 2024.

Cikin wata ƙididdiga da ya fitar a yanzu Naira na daidai da kuɗin Birr na ƙasar Habasha da kuma Fan na ƙasar Sudan a ɓangaren karyewa.

Rahoton ya ƙara da cewa buƙatar da ake samu na Dala a kasuwanni na daga cikin dalilin da ya sa Kuɗin ke karyewa .

A yanzu dai ana canza Dala ɗaya akan Naira 1700. Daga watan Agustan 2024, Naira ta faɗi da kusan kaso 43 cikin 100.

#bankinduniya #Najeriya #newmedia

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.