Sanata Barau Ya Jajantawa Al’ummar Jigawa

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, SP Barau Jibril Maliya ya jajantawa al’ummar Jigawa  bisa haɗarin tankar mai da ta yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 95 a Majiya dake ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar, DSP Shaidue Adam ya tabbatar da faruwar lamarin, inda mutane sama da 95 suka rasu, wasu kimanin 50 suka jikkata.

Sanata Barau cikin wata sanarwar da ya fitar ta bakin hadiminsa a ɓangaren yaɗa labarai, Isma’il Mudashir. 

Barau ya bayyana alhininsa da kuma kaɗuwarsa bisa abin da ya faru wa ga mutanen jihar Jigawa. 

“Cikin yanayi na tausayi da alhini, muna miƙa saƙon jaje ga gwamnatin jihar Jigawa da kuma al’ummar jihar, musamman al’ummar garin Majiya da wannan ifti’ai ya faru.

Muna addu’a ga mutanen da suka rasu da kuma addu’ar samun sauƙi ga mutanen da suka jikkata.” 

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda