Bene mai hawa daya da ake ginawa ya rushe a jihar Sokoto

 

Wani bene mai hawa daya da ake kan ginawa ya rushe a ranar Laraba a kan titin Bauchi da ke cikin birnin Sakkwato.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin rushewar ginin ba, sannan babu cikakken bayani kan ko akwai wadanda suka mutu ko suka jikkata sakamakon lamarin.

Hukumomin ba da agajin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Sai dai shaidun gani da ido sun ce mutane sun yi tururuwa zuwa wurin da ginin ya rushe, yayin da ake ci gaba da bincike.

Post masu alaƙa

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP