Hukumar wayar da kan jama’a kasa (NOA) ta yi Allah wadai da kalaman nuna wariya da wani dan sanda yayi.

Hukumar wayar da Kan jama’a kasa (NOA) ta yi Allah wadai da kalaman nuna wariyar kabila da ake zargin wani jami’in dan sanda ya yi ga wani direba a wani faifan bidiyoda ya yadu.

Hukumar ta ce kalaman da ake zargin jami’in ya yi na cewa da direban dan kabilar Igbo ne da ya mare shi, sun saba da ka’idojin hadin kan kasa da mutunta martabar kowane dan Najeriya.

NOA ta kuma yaba wa rundunar yan sandan Najeriya bisa gaggawar da ta yi wajen cafke jami’an da ake zargi tare da fara daukar matakan ladabtarwa a kansu.

Hukumar ta yi kira ga yan Najeriya su guji nuna wariya da kuma ci gaba da karfafa hadin ka da zaman lafiya a fadin kasar.

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun miƙa wa masu su motoci biyu da suka ƙwato tare da kama mutum Daya da ake zargi.

Bene mai hawa daya da ake ginawa ya rushe a jihar Sokoto

Kashi 70 na manyan laifuka a Kano na da alaƙa da shaye-shaye — Muhuyi