Rundunar yan sandan jihar Kano ta kwato motoci biyu da aka sace tare da mika su ga masu su, yayin da ta kama mutum daya da ake zargi.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Laraba, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon bincike da jami’an Special Intervention Squad (SIS) suka gudanar bisa samun bayanan sirri.
Sanarwar ta ce a ranar 26 ga Yulin 2026, wani mazaunin unguwar Hotoro mai suna Zaiyyad Farouk ya kai rahoton cewa an sace farar motarsa kirar Toyota Hilux mai lambar rajista KMC 25, bayan direbansa ya ajiye ta a kan titin Lamido Crescent da ke ƙaramar hukumar Tarauni.
CSP Kiyawa ya kara da cewa bayan samun rahoton, jami’an rundunar suka fara bincike, inda suka gano motar a hannun wani Abdussalam Salisu da ke unguwar Kurna Asabe a Kano, Inda aka ƙwato motar tare da miƙa ta ga mamallakinta.
Rundunar ta ƙara da cewa bincike na ci gaba domin cafke sauran waɗanda ake zargi da tserewa.
Haka zalika rundunar ta ƙwato wata baƙar motar Hyundai Elantra da aka sace a harabar Masallacin Annur da ke Abuja a ranar 10 ga Yulin 2026.
A cewar sanarwar, bayan samun bayanan sirri, jami’an SIS sun bi sawun waɗanda ake zargi har zuwa ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa.
Sai dai da suka hango jami’an ‘yan sanda, sun bar motar tare da tserewa.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargi na cikin wata ƙungiyar masu satar motoci da ke gudanar da ayyukansu a Abuja da jihohin Kaduna da Kano.
Kwamishinan yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen yaƙi da aikata laifuffuka.