Al’ummar unguwar Yakasai da ke cikin ƙaramar hukumar birni sun gamu da mummunan labarin kisan gilla da aka yi wa wani mai suna Jamilu.
Wakilinmu ya yi tattaki zuwa unguwar ta Yakasai, inda ya rawaito mana yadda ‘yan wannan unguwa ke nuna fushinsu kan yadda wannan al’amari ya faru da kuma yadda ayyukan daba ke cigaba da ta’azzara a unguwar ta Yakasai.
