Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bar Najeriya cikin kyakkyawan yanayi la’akari da cewa gwamnatinsa ta samu nasarori a fannoni da dama.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na ARISE, Sirika ya ce gwamnatin Buhari ta inganta tattalin arziki, ta rage matsalolin tsaro sannan ta shimfiɗa tubalin da gwamnatocin baya za su ci gaba da gini a kai.
Ya ce duk da ƙalubalen da gwamnatin ta gada, ta yi nasarar ƙwato ƙananan hukumomin da ƙungiyar Boko Haram ta mamaye, ta kuɓutar da wasu daga cikin ’yan matan Chibok, sannan ta bai wa manoma damar komawa gonakinsu.
Sirika ya kuma ce tattalin arzikin ƙasar ya kasance mai ƙarfi lokacin da Buhari ya sauka daga mulki, idan an yi la’akari ƙaruwa kuɗaɗen da ƙasar ke ajiya a ƙasashen waje, da kuma damar da masu zuba jari suka samu a harkokin kasuwanci.
Jawabin tsohon ministan na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin tunawa da shekara guda da rasuwar tsohon shugaba Buhari.