Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta ƙwato wata bindiga ƙirar Beretta, wata mota da ake zargin ta sata ce da wasu kayayyaki masu haɗari yayin wani samame da ta gudanar a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce a yayin samamen jami’an rundunar sun kuma kama motoci 123 da aka rufe masu lamba, aka lalata ko kuma marasa lamba, waɗanda ya ce masu aikata laifuka kan yi amfani da su wajen ɓoye ainihinsu.
A cewarsa, jami’an da ke Panshekara ne suka fara samun nasarar bayan sun tare wata mota mara lamba, inda direban motar, mai shekara 15, ya yi ƙoƙarin tserewa kafin jami’an su kama shi.
Bakori ya ce binciken da aka gudanar ya kai ga ƙwato bindiga ƙirar Beretta, tabar wiwi da ake zargi, wuƙa, batura 120 na lithium da kuma wata mota da ake zargin ta sata ce.
Ya ƙara da cewa an miƙa wanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), yayin da ake ci gaba da bincike domin gano asalin sauran kayayyakin da aka ƙwato.
Kwamishinan ya ce an gurfanar da direbobin motocin da aka kama a gaban kotu, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da irin waɗannan samame domin daƙile ayyukan masu aikata laifuka a faɗin jihar.