An Kama Wata Mata Da Zargin Safarar Makamai Zuwa Katsina
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da […]