An Kama Wata Mata Da Zargin Safarar Makamai Zuwa Katsina

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri.

Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune.

Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane na rundunar cikin gaggawa.

“Tawagar ta yi aiki tuƙuru, wanda ya kai ga kama wanda ake zargin tare da ƙwato alburusai 400 ƙirar 7.62ɗ39mm da harsashi 81 na 7.62mm na NATO.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “A yanzu haka ana tsare da wanda ake zargin kuma ana yi mata tambayoyi mai tsanani yayin da masu bincike ke ƙoƙarin tarwatsa cibiyar safarar makamai da kuma gano alaƙarta da ’yan fashi da makami da ta’addanci.”

Nansel ya bayyana cewa, kama matar yana wakiltar wani babban ci gaba a yaƙi da safarar makamai da aikata laifuka a yankin.

Post masu alaƙa

Hadejia ta cika shekaru 120 da cin nasara kan turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur