Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga 95 Tare Da Ceto Mutane 138 A Neja
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja. ’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai. Sojoji tare da taimakon jiragen yaƙi na sama sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri. Aƙalla ’yan ta’adda 95 […]