Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga 95 Tare Da Ceto Mutane 138 A Neja

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja.

’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai.

Sojoji tare da taimakon jiragen yaƙi na sama sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri.

Aƙalla ’yan ta’adda 95 aka kashe a yayin artabun.

Sojojin sun kuma lalata babura 18 tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47.

Sai dai an yi rashin sa’a soja guda ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar.

Dakarun sun sake kai wani farmaki na biyu inda suka ƙwato makamai da yawa tare da tarwatsa ’yan ta’addan.

Jama’a daga Warari, Rijau, da wasu ƙauyuka sun yi murnar nasarar sojojin suka samu.

Da yawa daga cikin mazauna yankunan sun tsere daga gidajensu saboda tsoro, amma sun dawo bayan ganin ƙoƙarin da sojoji suka yi.

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, an ga yadda jama’a ke taya sojoji murna da godiya.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa farmakin sojojin ya daƙile shirin kai hare-hare da ’yan ta’addan suka yi.

Wani mazaunin yankin shi ma ya ce ’yan ta’addan na shirin kai hari wasu ƙauyuka a Mariga, amma sun gudu bayan farmakin sojoji.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda