Ma’aikatan Da Ba Za A Biya Albashin Dubu 70 Ba
Karamin sashe na ɗaya na babban sashe na huɗu na dokar albashin Najeriya na 2019 da aka yi wa kwaskarima a 2024 ya ce biyan albashi mafi ƙaranci na naira dubu 70 bai shafi wasu ma’aikatu ba. Sashen ya lissafo su kamar haka: Ma’aikatun da ke da ma’aikatan wucin-gadi. Dillalai, waɗanda ma’aikatu ke biyan su […]