Majalissar Dattawan Nijeriya Zata Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro A Ranar Laraba
A gobe Laraba ne majalisar dattawa ta Najeriya za ta tantance sababbin manyan hafsoshin tsaron ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa. Tinubu ya aike da sunayen sababbin hafsoshin ne zuwa ga majalisa domin tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada. Shugaban majalisar Sanata Godwill Akpabio ya tabbatar da karɓar wasiƙar ta shugaban […]